<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>427</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Isowar Yesu a duniyan nan
 Al'ummai za su ji tsoro.
 Za su ce ma duwatsu da fannu,
 Ɓoye mu daga fuskarsa

[V2]
 KORUS
 Wannan ƙarshen ranar Allah ce.
 Wanene za ya tsaya a ranan nan, m'm,
 Ko kun tuba da toka a ranan nan, m'm,
 Za a ce babu dama .

[V3]
 2) Za ya  ce, &quot;Na aiko Yesu Kiristi&quot;.
 Ku kun ƙi ku karƃe shi.
 Kun giciye shi a bisa itace,
 Domin ba ku ƙaunarsa.
 Korus

[V4]
 3) Ni ma ranar ramawata ta zo.
 Zan saka ma kowa.
 Bisa gwalgwadon aikin da ya yi
 Da kuma ladansa.
 Korus

[V5]
 4) Ranan nan ba cewa, &quot;Ya Allahmu,
 Kai ka zalunce mu&quot;,
 Shi kuma za ya ce,  &quot;A'a mutane,
 Ni ban zalunce ku ba &quot;.
 Korus

[V6]
 5) Za ku ce &quot;Mun tubu, ya Allahmu&quot;
 Shi za ya ce, &quot;ba dama&quot;.
 Za ku ce, &quot;ka yafe mu, ya Allah&quot;.
 Za ya ce, &quot;babu dama&quot;.
 Korus

[V7]
 6) Za ye ce &quot;Jinin Yesu na ba da shi,
 Domin zunubanku.&quot;
 Wannan ya isa domin fansarku
 Ku kun ƙi bangaskiya. »
 Korus

[V8]
 7) Na gama, na gama, kun shiga wuta nan.
 Da na shirya ma Shaiɗan.
 Wayyo ! Allah mun shiga azaba.
 Ku kun shiga ba tausayi.
 Korus</lyrics>
<title>Isowar Yesu A Duniyan Nan LW427</title>
</song>